Abin tausayi: Gafiya ta cinye jariri dan wata 3
Wani abin al’ajabi da ban tausayi daya faru a kasar Afirka ta kudu ya dimauta mutane da dama, lamarin kuwa shine yadda wata gafiya ta cinye wani jariri mai watanni 3 da haihuwa gaba daya.
Jaridar Daily Mail ta ruwaito labarin, inda tace mahaifiyar jaririn yar shekaru 26 ta fita yawon dare ne zuwa wani gidan rawa, inda ta bar jaririn nata a gida. Jama’a da dama sun danganta laifin kisan yaron akan uwar tasa ballagaza.
KU KARANTA: Wata mata ta haifi ‘yan 4 a Sokoto
Wani makwabcin matar yace “a gaskiya jaririn nan yayi mutuwar wulakanci, domin mun tarar da gafiyar ta cinye masa idanu, harshe da yatsu, ba’a maganan sauran sassan jikin nasa da bamu gani ba. Sa’annan ga cizo daya sha a sauran sassan jikin nasa. Ya kamata ayi mahaifiyar daurin rai da rai, bata cancanci zama uwa ba”
Ita ma yar mai gidan da ballagazar mahaifiyar ke zama tace dama mahaifiyar jaririn bata sha’awar komai sai dai zuwa gidana rawa da karuwanci, wani sheda ya bayyana mana cewar ba wannan bane karo na farko da matar ke barin jaririn a gida ta fita yawo.
Sai dai Allah ya tseratar da dayan jaririn, dayake yan’biyu ne. dama dai matsalar yaduwar gafiyoyi a kasar Afirka ta kudu ya yawaita. A kwanaki ma an samu wata mata mai suna Nomathemba Joyi da gafiya ta cije ta a fuska yayin da take barci.
Asali: Legit.ng