Buhari ka sakar mana mara ko kuma…-matasan yankin Brass

Buhari ka sakar mana mara ko kuma…-matasan yankin Brass

- Mazauna Yankin Brass a jihar Bayelsa sun gargadi gwamnatin tarayya kan aniyarta na dauke masana’antar sarrafa isakar Gas daga yankin

- ‘Yan asalin yankin sun gudanara da wata zanga-zanga don nuna rashin amincewarsu dangane da aniyar hakan tare da barazanar a bin da ka iya biyo baya idan an ki

Buhari ka sakar mana mara ko kuma…-matasan yankin Brass
Matasan Brass na zanga-zangar dauke masana'antar sarrafa iskar daga yankinsu

‘Yan asalin yankin Brass ta Jihar Bayelsa, sun gudanar da wata zanga-zanga don nuna rashin amincewarsu da shirin gwamnatin tarayya na dauke masana’antar sarrafa isakar gas daga yankin.

Masu zanga-zangar su yi jerin gwanon nuna rashin amincewarsu da shirin na Gwamnatin Tarayya na yunkurin cire kaso arba'in nata, tare da sauyawa wurin sarrafa isakar gas din matsuguni.

KU KARANTA KUMA: Hoton bidiyon Dan Sanda na fada da direba ya janyo ka-ce-na-ce

Mazauna yankin sun yi kira ga Shugaba Buhari da ya fita daga al-amarin Jihar Bayelsa. Sun yi kuma kira ga gwamnan jihar Seriake Dickson da ya shiga tsakani.

Masu zanga-zangar da suka hada da mata da matasa dauke da kwalaye da aka rubuta: "Gwamnatin Tarayya ki rabu da wajen aikin gas na Brass a Bayelsa." Da "Buhari ka saurari mutanen yankin Niger Delta." da "Albarkatun iskar gas a Brass namu ne." Sai "Albarkatun iskar gas na Brass maganin matsalolin yankin Niger Delta ne." "Matasan yankin sun cancanci fiye da haka." "Ka bar albarkatun man gas da sauran albarkatu inda suke."

Wasu daga masu jerin-gwanon sun bayyana cewa shirin na Gwamnatin Tarayya, zai haifar da tashin hankali tare da rashin tsaro a yankin.

Sun kuma ce, suna tsoron kulle ma'aikatar zai jawo karuwar masu zaman kashe-wando a tsakanin matasan yankin.

Shugaban matasan Twon Brass mai suna Ebigon Sebo ya ce, "Shirin na Gwamnatin Tarayya na takalar fada ne."

Ya kara da cewa, "Aikin iskar gas na Brass zai iya tashi a kowane lokaci daga yanzu. "Sun kori ma'aikata a sakamakon shirin." Yanzu Gwamnatin Tarayya tana son tayi amfani da rashin aikin yi dan takalar mutanen yankin Niger Delta.

KU KARANTA KUMA: Ana shirin maido Ibori Najeriya

Idan aka cire wannan aiki zai jawo matasa su koma aikata laifuka. Muna rokon Gwamnatin Tarayya da ta kaucewa abinda zai jawo aikata laifuka da zubar da jini. Muna kuma gargadin cewa b aza mu kyale wannan aiki ya tashi tare da kayan aikin ba." Inji Sebo.

Sauran sun yi kira ga gwamnan jihar Seriake Dickson da ya shiga tsakani. Shirin na Gwamnatin Tarayya zai iya fusata al-umatai daban-daban na yankin.

"Idan aka dauke ma'aikatar gas ta Brass, mutane za su fusata, sannan sauran bukatun Gwamnatin Tarayya da ke da alaka da man fetur za su fada cikin garari." A cewar masu zanga-zangar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng