An kama ýansanda dumu dumu suna karbar cin hanci (Hotuna da Bidiyo)

An kama ýansanda dumu dumu suna karbar cin hanci (Hotuna da Bidiyo)

Wani ma’abocin kafar sadarwa ta Facebook ya tona asirin wani dansanda daya nemi ya bashi cin hanci, ko ace na goro daga hannunsu.

An kama ýansanda dumu dumu suna karbar cin hanci (Hotuna da Bidiyo)

Kamar yadda ma’abocin Facebook din ya bayyana, yace wasu jami’an rundunar yansandan jihar Legas su biyu ne suka tursasa musu lallai sai sun basu cin hanci yayin da suka kan hanyar tafiya.

Dayake ma’abocin Facebook din bai bayyana takamaiman inda lamarin ya faru ba, amma ya dauki bidiyon yansandan yayin da suke karban kudaden, kuma ya watsa shi a yanar gizo. Ga abinda yace:

KU KARANTA: Yan sanda sun cafke wanda ya kashe DSP Alkali a Rivers

“wannan labari da zan baku ya faru ne a gaban jami’ar jihar Legas dake Ojo, wasu yansanda ne su biyu suka rufe hanya, ta yadda dole sai direba yayi zagaye, amma da zarar direba ya shiga wannan zagayen, sai su cimma masa suce ya karya dokar hanya, don haka sai ya basu cin hanci.

An kama ýansanda dumu dumu suna karbar cin hanci (Hotuna da Bidiyo)

“duk da cewar fa a yanzu haka ana aikin gina hanyar ne, don haka ba wani abu bane idan direba ya juya, sunayen yansandan sune Chinedu da Roland. Ya zama dole ayi maganin yansandan nan. jama’a ku taimaka ku watsa bidiyon nan har sai hukumomin tsaro sun samu wannan bayani.

Sunan dansandan da hoton sa yafi fitowa a bidiyon nan Chinedu, sunan mahaifinsa Iwuka, sa’annan dansandan dake rike da Nokia X2 sunansa Rolanda."

Ku kalli bidiyon a nan:

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng