Rundunar Sojoji Dake Maiduguri Ta Ceto Mutane 1880 daga Dajin Sambisa
A cigaba da yakin da ta keyi da kungiyar Boko Haram rundunar sojojin Najeriya ta bakwai dake Maiduguri ta ceto mutane kimanin 1880 daga 'yan Boko Haram dake dajin Sambisa inda 'yan ta'adan suka yi kakagida tare da cafke wasunsu.
Mutane 1880 da sojojin suka ceto daga hannun 'yan Boko Haram sun hada da mata da kananan yara da tsoffi sakamakon fafatawar da su keyi da kungiyar ta'adancin a dajin Sambisa.
Kwamandan rundunar Manjo Janar Lucky Irabor yace baicin mutanen da suka ceto sun cafke wasu 504 da ake kyautata zaton 'yan kungiyar ta'adancin ne. Akwai kuma wasu 17 da suka mika kansu da kansu. Sun kuma kwato daruruwan shanu da 'yan ta'adan ke kwacewa daga hannun makiyaya a daji.
KU KARANTA KUMA: Mun koyi darasi, Inji Minisa Dalung
A kan raderadin cewa an kame shugaban Boko Haram Abubakar Shekau kwamandan yace shi ma haka ya ji amma bashi da tabbas saboda an ce wasu mafarauta ne suka kamashi. Yace yana jira ya san gaskiyar. Yace suna fatan hakan ya faru.
Kwanda Irabor yace babu 'yan matan Chibok cikin mutanen da suka ceto amma yace kura ta soma kaiwa 'yan ta'adan bango kuma nan ba da dadewa ba zasu ga karshensu tunda suna cigaba da aiki a dajin Sambisan.
Bugu da kari akwai wasu 'yan kasashen waje 37 da sojojin suka kubutar dasu. Zasu tantancesu su san ko suna cikin kungiyar ta Boko Haram. Duk wanda baya ciki zasu maidashi kasarsa ta asali.
Janar Irabor yace abubuwa da dama na faruwa kuma nan da sa'o'i 48 ra'a ji labari mai dadi. A halin yanzu dai sojojin sun fara shimfida hanya a dajin Sambisan da zai dinga basu damar shiga cikin dajin da sauki.
Asali: Legit.ng