Kwastam ta kama bingogi da alburusai a tashar jirgin ruwan Lagos

Kwastam ta kama bingogi da alburusai a tashar jirgin ruwan Lagos

- Hukuamar hana fasa kwabri ta kasa ta kama bindigogi da albarussai da aka boye su ne a cikin wasu motoci da aka shigo da su daga kasar Amurka

- Ta kuma kama wasu sundukan shigo da kaya kwatainoni 2 da makare da makamai da kuma kayayyakin soji da wani ya shigo da su a matsayin kayan gida

Kwastam ta kama bingogi da alburusai a tashar jirgin ruwan Lagos
Kwastam ta kama bingogi da alburusai a tashar jirgin ruwan Lagos

Hukumar hana fasa kwabrin ta yi shelar kama bindigogi samfurin da alabarusai da aka boye a cikin wata mota da aka shigo da ita daga kasar waje a tashar jirgin ruwa a Lagos.

Hukumar ta kuma sanar da kama makamai a cikin wasu kwantainoni guda biyu a tashar jirgin ruwa na Tin Can Island da ke Lagos.

KU KARANTA KUMA: An so a kai hari Gidan Shugaban MURIC

Jaridar Tribune ta rawaito cewa, Babban jami’in kwastam Yusuf Bashar da ke kula da tashar Tin Can, ne ya bayyana hakan a wani taro na manema labarai.

Mista Bashar ya ce, jami’ansa sun kama makaman ne a ranar 29 ga watan Nuwamba, shekarar 2016 sannan kuma an binkici kwantainonin ne a washegari sannan ya kuma ce,

“Da farko mun rike abin hawa da aka samu dauke da kunamun bindiga tare da albarusai masu carbi guda goma, a yayin da jami’anmu ke fita daga cikin Jirgin ruwa. Abin hawar mota ce kirar Toyota Corolla 2004 mai lambar bodi 2T1BR32E54C309841”

“Har zuwa yanzu dai ba a kama kowa ba tukunna, saboda mun gano lamarin ne a lokacin da ake fito da motocin daga cikin jirgin ruwa. Sai muna ci gaba da gudanar da binkice a kan mai motar ta yadda za mu gurfanar da mai laifin a gaban kuliya”.

Jami’in ya cigaba da cewa, “a kwantaina mai lamba MSCU718443/6 dauke da wata kuncen mta kirar Nissan Armada 2007 mai lambar bodi 5NIAA08A69N709779 muka gano wadannan abubuwan: bindiga kirar Omini American tactical rifle mai lamba AR48634 guda daya, da kuma wata guda dayan mai kirar Moaperg American pump Action rifle mai lamba U648018”.

Mista Yusuf ya kuma ce, “Kari a kan wannan bindigogi guda biyu, mun gano a dai cikin kwantainar wasu bindigun masu aiki da iska guda 3,500 samfurin Premier Hallow Point Airgun Pallet da kuma wasu Karin bundugun guda 4,000 masu samfuri iri daya”.

KU KARANTA KUMA: Shugaban Kasar Gambia yace ba wanda ya isa ya tube sa

A dai cikin kwantainar jami’an kwastam suka kama an samu hadadden abinci fakiti 26 domin amfanin sojoji, akwai kuma rigunan kariya daga harsashi ta sojoji guda 26,da hular kwano ta sojoji, da hular sojoji ta kare barkonon tsohuwa, da gilashin ido kwaya 2, da kuma takalmin sojoji guda biyu.

An kame wani da ake zargi na da hannu kuma ta ce za ta mika shi da kayan ga Hukumar tsaro ta farin kaya DSS domin kara gudanar da binkice.

Ku biyo mu a shafimun na Tuwita a @naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel