Kasar Jamus ta taimakawa Najeriya da kayan yaki (Hotuna)

Kasar Jamus ta taimakawa Najeriya da kayan yaki (Hotuna)

Gwamnatin Jamus ta bai wa Najeriya tallafin na'urar soji da kuma kudaden da suka kai Euro miliyan uku don yaki Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar. Tallafin dai ya hada da na'urar hangen nesa da kuma na'urar gano bama-baman da aka binne.

Kasar Jamus ta taimakawa Najeriya da kayan yaki (Hotuna)
Kasar Jamus ta taimakawa Najeriya da kayan yaki (Hotuna)

A jiya ne dai muka ruwaito maku cewar Ana zargin DPO na ‘yansanda ASP M. H Dass na Kiri a karamar hukumar Shelleng dake jiahr Adamawa da yiwa wasu matasa makiyaya hudu kisan mummuke.

Wannan na kunshe a wata takardar koke da ‘yanuwan mamatan suka gabatarwa kwamishinan ‘yansanda na jihar Adamawa Mal. Musa Kimo dauke da hotunan matasan lokacin da suke raye a caji ofis na Kiri da kuma na gawarwakinsu da aka yiwa daurin goro kwance kan uwar madatsar ruwa na Kiri.

Mahaifan wadanda aka kashe Mal. Kunuri Hampeto da Alhaji Bakari Kem sun shaidawa majiyar mu cewa bayaga gallazawa da barazana ga rayuwarsu lokacin da suka nemi DPO ya yi masu bayanin inda ‘ya’yansu suke, ya tozartasu biyan taran kudi sama da naira dubu dari shida da kuma shanu.

Mori Ori daya daga cikin wadanda suka sallake rijiya da baya da yanzu ke zaman gudun hijira na sama da watanni shida ya yi bayanin yadda ya kubuta ‘yan sa’o’i kamin ‘yan bangan Talum da DPO ya mika a hannunsu su kashe shi.

Ku biyo mu a tuwita: @naijcomhausa

Ku biyo a shafin fezbuk: Legit.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng