Babban abun mamaki da al'ajabi a kasar Jamus (Karanta)
Kungiyar RB Leipzig ta sake komawa mataki na daya a kan teburin Bundesliga na Jamus, bayan da ta ci Hertha Berlin 2-0 a ranar Asabar.
Timo Werner ne ya fara ci wa kungiyar kwallon kuma na tara da ya ci kenan a gasar ta Bundesliga ta bana, sannan mai tsaron baya, Naby Keita ya ci ta biyu.
Da wannan sakamakon, RB Leipzig, wadda ta shigo gasar Bundesliga a bara, ta bai wa Bayern Munich tazarar maki uku.
A wani labarin kuma, Manchester City ta doke Arsenal 2-1 a Etihad a wasansu na mako na 17 ranar Lahadi, abin da ya sa City ta zama ta biyu a tebur da maki 36, a bayan Chelsea mai 43.
Arsenal wadda ta fara cin kwallo a minti biyar kacal da shiga fili ta hannun Walcott, yanzu ta dawo ta hudu a tebur da maki 34.
Minti biyu da dawowa daga hutun rabin lokaci ne sai Leroy Sané ya rama wa Manchester City, kafin kuma a minti na 71 Raheem Sterling ya ci ta biyu.
Sai dai kuma zaman Mancester Cityn a matsayi na biyu zai iya zama na wucin-gadi kafin ranar Litinin, inda Liverpool za ta iya kawar da ita, idan ta yi nasara a gidan Everton.
Yanzu Arsenal ta maye gurbin Manchester City na da, matsayi na hudu a tebur.
Ku biyo mu a tuwita: @naijcomhausa
Ku biyo a shafin fezbuk: Legit.ng Hausa
Asali: Legit.ng