Wani kulob zai maida Mikel dan wasan da yafi kowa kudi

Wani kulob zai maida Mikel dan wasan da yafi kowa kudi

-Wata kungiyar kwallon kafa a kasar Faransa Olympique Marseille suna ta shirye shiryen sayen dan wasan nan na kasar Najeriya Mikel Obi a wata mai kamawa na sabuwar shekara.

-Kungiyar ta bayyana niyyar su ta mayar da dan wasan wanda yafi kowa kudi a kungiyar

-Shi dai dan wasan tuni ya ce zai tashi daga kungiyar sa ta Chelsea saboda mai horarwar baya son sa

Wani kulob zai maida Mikel dan wasan da yafi kowa kudi
Wani kulob zai maida Mikel dan wasan da yafi kowa kudi

Kulob din Olympique Marseille dake kasar Faransa sun bayyana aniyar su ta sayen jagoran tawagar yan kwallon Najeriya na Super Eagles a wata mai kamawa idan kasuwar cinikayya ta bude.

Kakar wasanni ta wannan shekarar dai bata zo wa dan wasan da kyau ba inda kawo yanzu dan wasan bai buga wa kungiyar kwallo ko daya ba saboda mai horar war basu da sawa da shi.

Mai karatu zai iya tuna cewa kawo yanzu dai dan wasan ya shafe shekaru 10 kenan a kungiyar.

A can kasar Jamani kuma, Kungiyar RB Leipzig ta sake komawa mataki na daya a kan teburin Bundesliga na Jamaus, bayan da ta ci Hertha Berlin 2-0 a ranar Asabar.

Timo Werner ne ya fara ci wa kungiyar kwallon kuma na tara da ya ci kenan a gasar ta Bundesliga ta bana, sannan mai tsaron baya, Naby Keita ya ci ta biyu.

Da wannan sakamakon, RB Leipzig, wadda ta shigo gasar Bundesliga a bara, ta bai wa Bayern Munich tazarar maki uku.

Ku biyo mu a tuwita: @naijcomhausa

Ku biyo a shafin fezbuk: Legit.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng