Gargadi ga ma’abota dandalin sada zumunta na Facebook
Ma’abota dandalin sada zumunta da muhawara na Facebook na cikin hadari idan suna kallon hotunan batsa.
Da wuya ba ka taba haduwa da wadansu rariyar wasu bayanai watau links ba a Facebook, da ake yi maka alkawarin wasu hotuna ko bidiyon batsa idan har ka danna su. To ka lura, wadannan ba komai bane face tarko.
Danna wadannan kafofin wata hanya ce da wasu mutane ke yaudarar jama’a domin ka sauko da wata manhaj mai hadari da za ta iya lalata maka waya ko Kwamfuta. Misalin irin wannan tallace-tallace na kwanannan shine wanda a ka yi alkawarin bidiyoyin batsa na Kim Kardishian, da Jessica Alba, da kuma wasu manya-manyan fitattun mutane.
Masu binkicen da suka gano wannan hanyar ta cutarwa ta kwanannan sun ankarar da jama’a.Hanyar na zuwa yawanci ta hanyar mahajjar Google Chrome wanda ya ke ta watsa shafukan a samfurin PDF na batsa, na sanannun mutane a Facebook.Idan a ka bude, PDF din zai kai wanda tsautsayin ya hada da shi, zuwa wani shafi feji da ke dauke da alamar hoton play. Idan a ka danna, to link din zai canza, ya kuma mayar da kai ka zuwa wani shafin da zai dameka da shigowar tallace-tallacen batsa da wasannin gyeyim. Bayan an danna, manhajar za ta bude shafin Facebook ya na alamar budewa.
Shi wannan abin yanzu zai iya karanta jerin sunayen abokanka da group dinka na Facebook da kuma wasu bayanai. Idan ka yi wasa, wannan abin da ke neman labari sai ya yi amfani da bayanan ka na Facebook ya tura wa duk abokanka da kuma group wannan rariyar din wanda yin hakan zai ba su dammar tallata hajar su da dama.
Wanda daga karshe kuma abin wannan ya hana garkuwar wayar ka ko compuer (antivirus) tasiri wanda daga nan komai ya zama barazana a garesu.Abu mai muhimmanci: ka kauracewa shiga kowane irin link da za a yi maka alkawarin hotunan ko bidiyon batsa ko da kuwa ka ga kamar ka san wanda ya turo maka.
Asali: Legit.ng