Dara taci gida : Boko Haram tayi barazanar kashe mabiyanta masu guduwa a filin daga
- Farmakin sojin Najeriya akan yan Boko Haram na haifan da mai ido a dajin Sambisa
- Kwamandan Operaion Lafiya dole,Manjo Janar Lucky Irabor, yayi kira da yan ta’adda su sallamar da kansu
Shugabannin Boko Haram sunyi arazanar kashe duk mambansu da ya gudu daga dajin Sambisa a yankin arewa maso gabas.
Wannan barazanar na zuwa ne bayan rundunar soji Najeriya na wura way an Boko Haram din wuta a dajin.
KU KARANTA: Dan achaba ya gamu da ajalinsa
Wani dan banga a Damboa, mai suna Malam Abubakar Buba ta tabbatar wa jaridar New Telegraph cewa shugabannin Boko Haram na gargadi ga mabiyansu.
“Daga labaran liken asirin da muke samu.wasu yan Boko Haram sun shiga hannun shugabanninsu, suna musu gargadi kada su gudu a filin fama ko a kashe su,”
Hakazalika, Kwamandan Operationlafiya dole,Manjo Janar Lucky Irabor, ya tabbatar da wannan barazanar da shugabannin Boko Haram din keyi.
Kana, Lucky Irabor, yayi kira ga yan Boko Haram su mika kansu a yanzu da suke daman yin hakan.
Yace rundunar soji zata kula da su sosai kuma game da hakkin dan adam.
Ku kasance tare da mu@ https://www.facebook.com/naijcomhausa, https://www.twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng