Matashi ya kashe mahaifiyarsa a jihar Ogun

Matashi ya kashe mahaifiyarsa a jihar Ogun

- Kanwar Segun ta kai kararsa ofishin yansanda cewa ya kashe mahaifyarsa wacce ta bace

- A yanzu haka an kai shi Eleweran a jihar Ogun bias ga umurnin kwamishanan yan sanda

Matashi ya kashe mahaifiyarsa a jihar Ogun
Matashi ya kashe mahaifiyarsa a jihar Ogun

Akwai wani tashin hankali da jami’an yan sandan jihar Ogun suke fuskanta a yankin kudu maso yammacin Najeriya.

Sun damke wani Segun Ogunlusi wanda ya hallaka mahaifyarsa, Abimbola Ogunlusi,kuma ya birne ta a salga,game da rahoton da jaridar Punch ta bayar na cewan wannan abu ya faru ne ranan Talata , 13 ga watan Disamba a Oketunde Street, Molatori, Ogijo,karamar hukumar Sagamu a jihar.

Kakakin hukumar yan sanda jihar, Abimbola Oyeyemi, ta tabbatar da cewa kanwar sa, Yetunde Ogunlusi,ta kai kara ofishin yan sanda.

KU KARANTA: ' Yan Najeriya basu ma Buhari Adalci

Yan sandan sune Yetunde ta bayyana cewa mahaifyarsu ta bar gida lokacin da take zuwa aiki ranan Talata,13 ga wata Disamba,2016 kuma da ta dawo, bata ganta ba.

Oyeyemi tace:“Ta kara bayyana cewa lokacin da ta tambayi yayanta,Segun, wanda ke tare da mahaifiyar a gida, abin da ya fada mata bai gamsar da ita ba.

“Bias ga rahoto, shugaban yan sandan yankin Ogijo ,Ahmed Tijano,ya jagoranci yan snada zuwa gidan da ke Oketunde , Molatori, Ogijo, kuma aka damke shi.”

A lokacin binciken, yan sanda sun bayyana cewa Segun ta kashe mahaifiyarsa kuma ya birne ta a salgan da ke kusa da gidan.

Ku kasance tare da mu@ https://www.facebook.com/naijcomhausa, https://www.twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng