Bazawara tayi ma saurayinta tofin Allah tsine bayan ya rabu da ita, ya auri budurwa

Bazawara tayi ma saurayinta tofin Allah tsine bayan ya rabu da ita, ya auri budurwa

Wata mata bazawara Joke Afolabi ta nuna bacin ranta a shafukan sadarwa na zamani sakamakon yaudarar ta da tace sauryinta yayi bayan tsere ya auri budurwa.

Bazawara tayi ma saurayinta tofin Allah tsine bayan ya rabu da ita, ya auri budurwa
Saurayin da Amaryarsa

Bazawarar ta taya shi murna, sai dai da biyu ta mai wannan murna, saboda ce mai tayi “ina ma saurayina murnan bikin aurensa, amma fa ka sani, babu yadda za’a yi ka lalata rayuwar wani, kuma kai kayi rayuwa mai kyau. Tsinannen mayaudari Akinmesere Martins Seyi.”

KU KARANTA:Farashin kayan abinci ya karye a jihar Legas

Bazawara tayi ma saurayinta tofin Allah tsine bayan ya rabu da ita, ya auri budurwa

Sai dai bayan labarin ya isa kunnen Saurayin, kuma har ya mayar mata da martani, sai Bazawarar ta kara cewa, “ai na san baka da hankali, don me zaka dami matar da ka san tana daukan nauyin yaranta da duk wani dawainiyarsu?

“Kai da wulakanta yaronka, baka taba bashi kulawa ba ko sau daya, tunda muka haife shi 15,000 kacal ka taba kashe masa. Don haka ba zaka taba samun kwanciyar hankali a gidanka ba. Ina so ka biyani 40,000 dina daka ranta, matsiyaci kawai.”

Bazawara tayi ma saurayinta tofin Allah tsine bayan ya rabu da ita, ya auri budurwa

Fatan mu a nan shine a samu sulhu tsakanin mutanen nan, ko dan yaronsu.

Ku cigaba da bibiyan labaran mu a nan, ko a nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel