Wani fasto ya so yin tafiya saman ruwa; sai mai afkuwa ta afku
1 - tsawon mintuna
Da alama dai abun dariya bai karewa dangane da fastoci a wannan zamani don kuwa wasu sun dage kan lalle sai sun yi wani abun al'ajabi ga mabiyan su don su kara gasgata su.
Wasu daga cikin su dai yanzu haka sun fara halaka kansu don ganin sun cimma burin nasu. Hakan ya sa wasun su suke ta jefa rayuwar su cikin hadari.
A kwananan wani fasto ya nutse a cikin ruwa lokacin da yake son nunawa mabiyan sa cewar shi fa babban fasto ne kuma ya sha banban da sauran a kasar Afrika ta kudu.
Kafin faruwar wannan ma dai a kwanakin bayan har ila yau wani faston shima ya nutse lokacin da yake son ya kwaikwayi Yesu wajen tafiya saman ruwa.
Faifan bidiyon:
Ko mi ke sa su yin wannan kasadar?
Asali: Legit.ng