Bikin Maulidi: Yan shi'a sun mamaye garin Katsina

Bikin Maulidi: Yan shi'a sun mamaye garin Katsina

Daruruwan mabiya kungiyar nan ta 'yan uwa musulmi wadda Zakzaky ke shugabanta ta gudanar da gangamin bulin maulidi a garin Katsina don tunawa da zagayowar haihuwar manzon Allah SAW.

Bikin Maulidi: Yan shi'a sun mamaye garin Katsina
Bikin Maulidi: Yan shi'a sun mamaye garin Katsina

Mai rahoton mu dai ya ga da yawa daga mabiyan sun yi shiga ta kaya iri daya na bakaken kaya suna wucewa ta Filin Samji zuwa Kofar Soro.

A jawabin sa a ranar, mukaddashin shugaban kungiyar Mallam Yakubu Yahaya ya kara nanata bukatar su ta ganin an sako shugaban su na kasa Ibrahim Zakzaky a cikin wa'adin kwanakin da aka dibar ma gwamnati.

Shugaban har ila yau ya kara kira ga mabiyan su da su ci gaba da zama lafiya da sauran al'umma tare da ci gaba da nuna bukatar su ta ganin an sako masu shugaban su.

Majiyar mu ta tabbatar da cewar duk da cewar an dage dokar nan ta hana zagaye a jihar, amma jami'an tsaro sun mamaye manyan titunan garin don tabbatar da bin doka da oda da kuma tabbatar da kaucewa duk wani hadari ko wane iri ne.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng