Za’ayi bikin auren yarinyar Sarkin Kano Muhammadu Sunusi
1 - tsawon mintuna
Sarkin Kano mai martaba Muhammadu Sunusi zai bada auren yarsa Gimbiya Fulani Siddika a wannan watan Disamba.
KU KARANTA:An gano wani yaro da aka boye shi a cikin bango a garin Akure
Za’ayi bikin auren gimbiya Fulani Siddika a ranar juma’a 23 ga watan Disamba, don a yanzu haka har an fitar da takardan gayyata, wanda aka fara raba ma jama’a, yan’uwa da abokan arziki.
Angon Gimbiya Siddika shine Malam Abubakar Umar Kurfi.
Za’ayi waliman auren a fadar mai martaba Sarkin Kano.
Ku bibiye labaran mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa
Asali: Legit.ng