‘Yar kasuwa ta ci miliyan daya a gasar Red Hot Promo na Airtel

‘Yar kasuwa ta ci miliyan daya a gasar Red Hot Promo na Airtel

Kusan mako daya kenan da Babban Kamfanin sadarwar nan na Kasar nan Airtel ya kaddamar da Gasar Red Hot Promo, wannan ne dai karo na hudu da Airtel din ta gudanar da wannan tsari; wanda yana daga cikin mafiya inganci a Najeriya. Yanzu haka dai, mutane da dama daga sassa na Kasar nan sun lashe kyaututtuka iri-iri dabam-dabam.

‘Yar kasuwa ta ci miliyan daya a gasar Red Hot Promo na Airtel
‘Yar kasuwa ta ci miliyan daya a gasar Red Hot Promo na Airtel

Misis Kemi Siwoku; wata ‘yar kasuwa mai shekaru 48 a Legas ta samu lashe gagarumar kyautar Miliyan daya. Sannan kuma mutane 20 sun samu cin kyautar N100,000. Ba a nan kadai wannan abu ya kare ba, Mutane har 18,000 sun samu kyautar katin waya wanda ya kai na Naira Miliyan Tara daga ranar 6 zuwa ranar 8 ga Watan Disamban nan.

Wannan ‘yar kasuwa watau Misis Siwoku ta nuna matukar jin dadin ta da kuma godiya da Kamfanin Airtel da suka saka mata da sauran Jama’a da wannan kyauta ta tsarin Red Hot Promo.

‘Ina jin abin kamar a mafarki…na kidime…lallai na kare Shekarar 2016 da kafar dama…’ Misis Siwoku ta ke fada tana mai cike da farin ciki lokacin da Airtel su ka kira ta.

Airtel tace mutane fiye da 360,000 za su ci kyaututtuka dabam-dabam wannan shekarar, shi ya sa Gasar banan ta fita dabam daga wadanda aka taba yi a baya, shekaru hadu da suka wuce.

A wannan Gasa na Airtel Red Hot Promo na shekarar bana 2016, Airtel din za su raba kyaututtuka na kudi kusan Naira Miliyan 200. Mutane 8 masu rabo za su samu kyautar Naira Miliyan goma watau N10, 000,000 kowanne. Mutane 60 kuma za su ci Naira Miliyan guda.

A cikin watanni biyu dai, za a samu mutane 600 da za su lashe kyautar N100,000. Haka kuma mutane 360, 000 za su samu kyautar katin waya na N500. Hakan na nufin mutane fiye da 360, 000 za su karu da Gasar na bana.

Ga mai son shiga Gasar don a buga da shi, sai a saye kati a layin Airtel na kira ko shiga yanar gizo, a latsa *340# domin a kutsa. Iya kudin ka, iya shagalinka…

Wanda duk ya fi saka katin waya, shi ne ke kan gaba a Gasar. Ga mai son ganin matakin da yake bayan ya shiga Gasar sai ya aika sako ‘POINTS’ ga Lambar 340. Wannan sako kyauta ne. Za a ci gaba da wannan Gasa har 3 ga Watan Faburairun 2016.

Asali: Legit.ng

Online view pixel