Rudani a gidan soja yayin da manyan hafsoshin Sojan Nijeriya 2 suka bukaci ritaya

Rudani a gidan soja yayin da manyan hafsoshin Sojan Nijeriya 2 suka bukaci ritaya

Shugaban Kasa, Muhammad Buhari ya amince da takardar yin ritaya da Shugaban Hafsoshin Nijeriya, Janar Gabriel Olonisakin da kuma Shugaban rundunar Sojan Ruwa, Vice admiral Ibok- Ete Ekwe Ibas suka mika masa.

Rudani a gidan soja yayin da manyan hafsoshin Sojan Nijeriya 2 suka bukaci ritaya
Rudani a gidan soja yayin da manyan hafsoshin Sojan Nijeriya 2 suka bukaci ritaya

Tuni dai ministan tsaro, Mansur Dan Ali ya nemi manyan hafsoshin kan su mika ragamar iko ga wadanda ke bin su a mukami wanda kuma ake sa ran Shugaban Rundunar Sojan Sama, Air Marshal Abubakar Sadik ne zai maye gurbin Shugaban hafsoshin Nijeriya a matsayin na riko kafin Shugaba Buhari ya yi sabon nadi.

A wani labarin kuma, Hukumar kula da tabbatar da da'ar ma'aikatan Najeriya watau CCB ta sha alwashin yin bincike a cikin karar da aka kai mata ta cewa shugaban sojin Najeriya Tukur Buratai ya yi karya wajen bayyana wasu kadarorin sa ga gwamnati.

Shi dai Buratai ya shiga matsala ne tun bayan da aka gano cewar wai yana da wasu kadarori a garin Dubai.

Hukumar sojin da bata musanata batun ba inda tace amma kadarorin nashi ya samesu ne ta halaliyar hanya indakuma suka ce ya bayyana su a cikin takardar sa ta aiki.

Sai dai daga baya wata kungiyar farin kara ta bukaci hukumar ta CCB da ta binciki shugaban sojojin sannan kuma ta hukunta shi idan har ta same shi da laifin.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng