An gano wani yaro da aka boye shi a cikin bango a garin Akure

An gano wani yaro da aka boye shi a cikin bango a garin Akure

Rahotanni sun ruwaito labarin wani yaro da aka ceto rayuwarsa wanda aka gine shi a tsakan kanin buloluka a jikin wani bango a garin Akure, babban birnin jihar Ondo.

An gano wani yaro da aka boye shi a cikin bango a garin Akure
Yaron da aka gano a cikin bango

Yanzu haka jami’an tsaro sun baza komar suna neman mamallakin gidan bulon da aka gano yaron ruwa a jallo.

Tun misalin shekaru biyar ne da suka gabata iyayen wannan yaro mai shekaru 12 suka cire rai daga neman yaron nasu bayan ya bace, kuma an neme shi an rasa.

An gano wani yaro da aka boye shi a cikin bango a garin Akure

KU KARANTA:Madam Ngozi ta nisanta kanta da jita-jitar takara a 2019

An ceto yaron ne a wani gidan buga bulo dake titin Oduduwa, yankin Ijapo na garin Akure bayan an ji muryarsa yana taw aka cikin dare har na tsawon kwanaki uku.

Da aka tuntubi iyayen yaron, sai suka ce wasu bokaye a baya sun fada musu cewar matsafa ne suka yi amfani da yaron, don haka su daina bata lokacinsu wajen neman shi. Jama’a da dama sun tausaya ma wannan yaron, tare da al’ajabin yadda aka gine shi da kuma yadda ya rayu duk tsawon shekarun nan.

Wani majiyar mu, wanda shima boka ne ya bayyana mana cewar kiranye matsafa suka yi ma yaron, kuma ya shafe shekaru 5 a cikin wannan hali, sa’annan suna ciyar dashi jinin mutum da naman mutum daga duniyarsu irin ta matsafa.

Majiyar namu ya shawarci iyayen yaron dasu mika shi ga hannun manyan bokaye don su dawo da shi yadda ya kamata, saboda a yanzu haka sun canja shi.

Zaku iya samun labaran mu a shafin Tuwita @naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng