Sa’idawa! An gayyaci Gwamna El-Rufai sa ido a zaben kasar Ghana
1 - tsawon mintuna
Rahotanni sun ishe mu a yanzu haka Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai na kasar Ghana don sanya idanu akan yadda zabukan kasar zasu kasance.
An fara gudanar da zaben shugaban kasar Ghana tun a jiya Laraba 7 ga watan Disamba, inda akwai manyan yan takara guda biyu, da suka hada da shugaban kasa John Dramani Mahama daga jam’iyyar NDC, da shugaban yan hamayya Nana Akufo-Addo daga jam’iyyar NPP.
Sauran yan takaran kujerar shugaban kasar Ghana sun hada da Ivor Greenstreet na jam’iyyar CPP, sai kuma Paa Kwesi ndoum na jam’iyyar PPP.
Ga sauran hotunan gwamnan a Ghana.
Asali: Legit.ng