An sallami ma’aikata 109 daga kamfanin Dangote, suara na jira

An sallami ma’aikata 109 daga kamfanin Dangote, suara na jira

Sakamakon matsalar karayar tattalin arziki, kamfanin Dangote ta sallami ma’aikatan kamfanin siminti dake Obajana, jihar Kogi su 109.

An sallami ma’aikata 109 daga kamfanin Dangote, suara na jira

Daraktan dake kula da manyan motocin kamfanin Dangote Abdullahi Magaji ya bayyana haka a ranar Talata 6 ga watan Disamba a farfajiyar kamfanin siminti na Obajana.

Jaridar Vanguard ta ruwaito Magaji yan fadin cewar mutanen da aka sallama suna cikin wadanda aka kama da laifuka daban daban, da suka hada satan kaya, daukan kaya ba aka ka’ida ba da makamantan laifukan da suka ci karo da dokokin kamfanin.

KU KARANTA: Hukumar Kwastam tayi babban kamu

Magaji yace sauran ma’aikata 115 na jiran a kammala bincike akan su, yayin da suke tsare a gidan yari.

Yace: “Ina farin cikin bayyana muku mun kama barayin tare da gano motoci 5 da aka sace mana, sai dai an riga an sace kayayyakin motocin. Bugu da kari mun samu nasarar kama wani Samaila Yakubu, wanda yak ware wajen satar motocin mu tare da hadin bakin wasu direbobi.

An sallami ma’aikata 109 daga kamfanin Dangote, suara na jira

“Wadannan sune gungun barayin da suka addabi motocin mu a yankin kudu maso gabas da kudu maso kudu.”

Magaji yace Alhaji Aliko Dangote ya basu umarnin dole suyi maganin yawan sace sace da ake samu a kamfanin. Yace: “Muna manna takardan gargadi a jikin motocin mu, inda muke hana direbobin mu daukan fasinja ko kaya, inda banan kamfanin mu bane.

“Da wannan muke bukatar jami’an tsaro dasu tallafa ma kamfanin Dangote wajen kama masu laifi cikin ma’aikatansu.”

Zaku iya samun labaran mun a shafin Tuwita @naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng