Kalli yadda Minista Dalung yayi ma burodi da wake cin yunwa (HOTUNA)

Kalli yadda Minista Dalung yayi ma burodi da wake cin yunwa (HOTUNA)

Wasu hotunan Ministan matasa da harkar wasanni sun watsu a yanar gizo lokacin dayake cin abinci yayin daya kai ziyara a sansanin masu yi ma kasa hidima.

Kalli yadda Minista Dalung yayi ma burodi da wake cin yunwa (HOTUNA)

Su dai yan yi ma kasa hidimar an killace su ne tun a watan daya gabata, sa’annan za’a sako su a ranar 14 ga watan Disambar bana, inda daga nan zasu wuce zuwa inda za suyi ma kasa aiki.

A cikin hotunan an hangi Minista Dalung yana cin burodi da wake, wanda aka dafa ma matasa yan yi ma kasa hidimar don ya tabbatar da ingancin abincin da ake dafa musu.

KU KARANTA:Yawan cin Kilishi, Balango da Farfesu ke kashe Ýan Najeriya

Ga sauran hotunan nan:

Kalli yadda Minista Dalung yayi ma burodi da wake cin yunwa (HOTUNA)
Kalli yadda Minista Dalung yayi ma burodi da wake cin yunwa (HOTUNA)

Idan ba’a manta ba, a baya, Dalung ya sha suka kakkausa daga wasu yan Najeriya lokacin da aka nada shi ministan wasanni, saboda suna ganin shi bako ne a harkar wasanni a kasar nan.

A wani labarin kuma, yan Najeriya sun yi kiraye kiraye da a soke shirin yi ma kasa hidima (NYSC) sakamakon mutuwar yan yi ma kasa hidima har guda Uku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel