Wata mata taci dukan tsiya saboda tayi zina da mijin wata
Wata mata yar Najeriya da ba'a bayyana ko wacece ba an mata bugun kawo wuka bayan da aka samu rahoton tana zina da mijin wata matan aure.
A cewar wani ma'aboci amfani da kafar sada zumunci na Facebook mai suna Shaguolo Clemmy Elohor, matashiyar dai an mata dukan tsiya da yima rayuwarta barazana a lokacin da mutanen unguwarsu suka kamata da laifin da ake ikirarin ta aikata.
KU KARANTA: Ana shirin haramta amfani da Hijabi
Ya dai rubuta cewar anyima fuskar ta zane da wuka inda akaji mata ciwuka sosai saboda tana neman mijin wata mata, Don hakane yasa sukayi mata wannan mummunar hukuncin. Kuma na tabbata mutumin baice komai ba, saboda yasan cewar ya aika zinan.
Duk wa'Annan mazajen dake bin yan mata a waje, suna barin matan su da kuma yaran su a gida suna cema matan wai matansu na gida basu kaisu ba. To yanzu saisu kalli abin da ya faru da wannan yarinyar. Mu mata garin neman kudin mune muke kai kanmu mu baro.
Allah ya kyauta!
Ku biyomu a shafinmu na tuwita @naijcomhausa
Asali: Legit.ng