Abun mamaki a yayin da wata Kansila tayi aure a gurin tsafi

Abun mamaki a yayin da wata Kansila tayi aure a gurin tsafi

Wata mata kansila tabar cece kuce a yayin da ta auri mijin ta a gurin yin tsafi wanda wani boka ya daura.

Kamar yadda muka samu rohoto daga kasar Uganda sannanar kansilar Ruth Nakamatte tayi aure da mijin ta Buyondu Manyigaaluubale a gurin wani tsafi a kauyen su, biki na cire raini.

Shugabanin  bokayen kauyen(Kaboma Jjumba da Kaboma Kayondo Nyongaraako) suka daura auren a kasar Uganda ranar lahadi 5 ga watan Disamba , duk da bikin ya kawo cece kuce amma kansilar tayi kunnen uwar shegu.

Abun mamaki a yayin da wata Kansila tayi aure a gurin tsafi

Nakammate an taba mata wankan batisma inda aka bata suna Ruth, sai dai bata bi ka'idar addinin ba inda tazo da kanta gurin bokaye dan yin aure, kuma ita ta fara shiga gurin da yake cike da bokaye da mabiyan su.

KU KARANTA: Wani sanannen Fasto ya bugi kirjin cewa ana tsoron sa.

Nakamatte ta iso gurin da fararen kaya, kafin tazo ta canza ta saka na gargajiya, ba kamar yadda muka sani ba ne a baya inda bokaye suke aiki da dare, amma wadan nan tsakar rana su yi nasu.

Kuma sun gayyatu masu kidin gargajiya inda suke yin waka a cikin nishadi da kuma yabon al'afdin su.

Abun mamaki a yayin da wata Kansila tayi aure a gurin tsafi

Su dauki alkawalin auren su da kyau in suka ce sai mutuwa zata raba su daga auren da Jjumba Kabina.

Ku biyo mu a shafin mu na tuita @naijcomhausa. 

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng