Wani Saurayi ya harbe matar aure, saboda bata son shi
Wani saurayi ya harbe wata matar aure mai dauke da juna biyu da yake nema yayin da take taka rawar banjo a wani taron bikin aure bayan ta ki amsa mai soyayyarsa.
Gidan talabijin NDTV na kasar India ya ruwaito labarin kashe bazawarar mai shekaru 25 mai suna Kulwinder Kaur, rahoton yace Saurayin Kulwinder ne ya harbe ta a ciki yayin da take tsakar rawa a wani bikin aure a garin Punjab Bathinda a ranar Asabar, 3 ga watan Disamba.
KU KARANTA: Messi ya baiwa ýaýan Barack Obama babban kyauta
Mijin Kulwinder, Harjinder Singh yayi ikirarin cewar wani mutum mai suna Billa ne ya harbi matar tasa, wanda acewar Singh dama ya dade yana neman ta.
“Tun da aka fara bikin suke damunta data dawo ta zauna kusa dasu, amma ta ki, daga nan ne suka harbe ta, inji mijinta Singh. Kulwinder ta kasance mai sana’ar rawar nanaye ne a wata kungiyar rawa, wanda suka zo garin Maur Mandi don yin rawa.
“Sai dai wani jami’in dan sanda Daljit Singh yace mutumin daya harbe kulwinder ba da gangan ya harbe ta ba, yace kuskure aka samu, amma zaku samu isashshen bayani bayan an kammala bincike akan gawarta.”
A yanzu haka dai jami’an tsaro sun bazama neman wanda yayi harbin, Billa, yayin daya tsere bayan Kulwinder ta mutu.
Su ma shaidun gani da ido sun bayyana cewar Kulwinder na cikin rawa ne sa’adda Billa ya harbe ta. Tuni an mika gawar Kulwinder asibiti, inda aka tabbatar da mutuwarta.
Zaku iya samun labaran mu a shafin Tuwita @naijcomhausa
Ga bidiyon harbin
https://youtu.be/MClUsppSA40
Asali: Legit.ng