Tsagerun Neja Delta zasu kuka da kansu

Tsagerun Neja Delta zasu kuka da kansu

- Gwamnatin Najeriya na samarwa da rundunar sojojin ruwan kasar manyan jiragen yaki na zamani

- Yanzu haka dai gwamnatin tarayya na ci gaba da mayar da hankali wajen samar da jiragen ruwan yaki ga rundunar ruwan sojojin Najeriya. A karo na biyu katafaren jirgin yakin da Najeriya ta sayo daga kasar China, ya isa kasar Angola kan hanyarsa ta zuwa Najeriya

Tsagerun Neja Delta zasu kuka da kansu
Tsagerun Neja Delta zasu kuka da kansu

Daraktan watsa labarai a hedikwatar sojojin ruwan Najeriya, Komanda Christan Ezekobe, yace rundunar sojojin ruwan Najeriya suna ci gaba da samun manyan jiragen yaki irin na zamani da ake ji da su a wannan karni. Ya kuma ce jirgin farko ya isa Najeriya a bara, wannan kuma gashi yana kan hanya, wanda idan aka kaddamar da su zasu taka rawa sosai wajen samar da tsaro ta cikin ruwa.

Tsagerun Neja Delta zasu kuka da kansu

KU KARANTA: Shugaban Najeriya ya maidawa sarki sanusi raddi

Yanzu dai sojojin ruwan Najeriya zasu fara sintiri har zuwa gabar kotun Guinea. A cewar kwararre kan sha’anin tsaro Kwamanda Ahmed Tijjani Baba Gamawa, aikin sojojin ruwa ne su kula duk wani abu dake faruwa ta cikin ruwa, wanda kuma ya hada da matsalar da ake samu a yankin Niger Delta inda ake fasa bututun mai ana kuma satar danyen Mai.

Tsagerun Neja Delta zasu kuka da kansu
Nigerian Navy personnel guarding the territorial waters of the country

Hakan yasa shugaban kasar Najeriya Mohammadu Buhari, yayi aniyar kara musu karfi ta hanyar samarwa rundunar jiragen zamani don samar da tsaro ga jiragen dake sintiri ta kan ruwan kasar.

A wani labarin kan tsaro kuma, Rundunar sojin Najeriya ta ce wani jami'inta ya harbe wata mace 'yar kunar-bakin-wake da ta yi yunkurin tayar da bam a jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar.

Wata sanarwa da kakakin rundunar sojin kasa, Kanar Sani Usman Kukasheka ya aikewa manema labarai, ta ce an harbe matar ne a yayin da take yunkurin shiga wani sansanin soji da ke Yamtake a karamar hukumar Gwoza.

A cewarsa, hakan ya faru ne jim kadan bayan soji sun dakile wani hari da 'yan ta'adda suka yi yunkurin kai wa.

Sanarwar ta ce sojojin sun kashe maharan guda hudu, cikinsu har da 'yan kunar-bakin-wake biyu sannan suka kwace bindigogi da alburusai da kuma miyagun kwayoyi daga wajen su.

Sai dai Kukasheka ya kara da cewa soja daya ya rasa ransa a lokacin ba-ta-kashin.

A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa

&feature=youtu.be

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng