Wata yarinya ta yi hakan

Wata yarinya ta yi hakan

Wata yar shekara 24 mai suna Lin Shuping, har yanzu tana daukar cewa ita sabuwa ce fil a leda bata taba saduwa da wani namiji ba, duk da haihuwar da tayi a wata asibitin kasar China farkon watan Nuwamba. 

Lin Shuping yar shekara 24  tace bata da Saurayi kuma bata taba sanin wani da namiji ba, a lokacin da ake tambayar ta yadda akayi ta samu ya mace.

Lin tace bata da masaniyar haka.

Wata yarinya ta yi hakan

A safiyar 16 ga watan Nuwamba, ta fadi bagatatan sai aka kai ta asibiti, sai dai mamaki ya cika ta a lokacin da taga an shiga da ita dakin haihuwa, wanda bata da wata masaniyar tana da ciki, duk da watanni 9 da ta shafe bata ga jinin al'ada ba.

KU KARANTA: Shirin N-power zai iya fitar da Najeriya halin tabarbarewa tattalin arziki.

Sai dai abun takaici Lin ta samu ciki da bata sani ba, wanda abun mamaki ne.

Tace ita bata da kudin da zata dauki nauyin wata jaririya dan haka tana son ta bar jaririyar.

A asibitin kuma suna ta kokarin neman iyayen ta dan a Guangxi dan suzo su biya kudin magani dan bata da abun biya.

Ku biyo mu a shafin mu na tuita @naijcomhausa. 

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng