Sojojin ruwan Najeriya za su sa kafar wando daya da tsageru
Babban hafsan manufofi da tsare-tsare na rundunar sojojin ruwan Najeriya Real Admiral Joseph Ajani yace kimanin jiragen ruwa sama da tamanin da jirage masu saukan ungulu za'a yi atisahin dasu da aka sama lakani "Idon Mikiya."
Real Admiral Ajani yace rundunar sojin kasar ta musamman dake yaki a doron kasa da cikin ruwa da sojojin sama da ma jami'an tsaron farin kaya duk zasu tsunduma zuwa yankin na Niger Delta domin gagarumin atisahin.
Rundunar sojin ruwan Najeriya tace tsagerancin 'yan bindigan Niger Delta tamkar kalubalantar karfinta ne.
KU KARANTA: Ana dab da samun riga-kafin cutar kanjamau
Kwamandan watsa labarai na hedkwatar rundunar sojojin ya bayyana hikimar yin atisahin. Yace rundunar sojin ruwa kodayake ita ce zata yi jagoranci amma ba zata ce aikinta ba ne ita kadai. Tana bukatar hadakan sauran sojojin da jami'an tsaro.
Wani masanin tsaro Ahmed Tijjani Babagamawa acewarsa atisahin nada alfanu saboda zai ba sojojin ruwan karin fahimta da yadda zasu sarafa sabbin kayan yakinsu. Yace dole ne a yi atisahin a yankin ganin irin halin da ake ciki.
Shi ma Dr. Abubakar Umar Kari malamin jami'ar Abuja yace matakin ba sabon abu ba ne. Yace wannan abun da ake cewa "a tauna tsakuwa domin aya ta ji tsoro". Yace ana cewa ana tattaunawa ta ruwan sanyi amma su 'yan tsageran basu daina abubuwan da suke yi ba. Da wannan atisahin mai yiwuwa zasu shiga taitayinsu inji Dr Kari.
Asali: Legit.ng