Ta rubuta Al-Qur’ani gaba daya da tawadan ruwan Zinari
Idan mutum ya gamsu da addininsa, ba abinda zai gagareshi yi ma addinin nasa.
An samu wata kasaitacciyar marubuciya yar kasar Azerbaijan mai suna Tünzale Memmedzade data rubuce Al-Qur’ani gaba daya, bango zuwa bango da tawadan ruwan Zinari da na Azurfa.
Wannan lamari na Marubuciyar nan yayi matukar daukar hankalin al’ummar Duniya gaba daya, saboda mamakin yadda ta kwashe shekaru 3 tana gudanar da wannan aiki.
KU KARANTA:An dambace tsakanin Gwamna da dan majalisa
Baya da amfani da tawadan ruwan Azurfa da Zinari, Marubuciya Tünzale Memmedzade tayi amfani da kyallen Siliki a matsayin fallen takardan rubutun. Malama Tünzale Memmedzade mai shekaru 33 tace dalilinta na yin wannan aikin shine sakamakon an rubuta Qur’ani akan abubuwan rubutu daban daban, amma ba’a taba rubuta shi ba a kan kyallen Siliki.
Sai dai Malama Tünzale Memmedzade tayi amfani da samfurin Qur’ani bugun kasar Turkey, wanda ma’aikatan kula da al’amuran addinin musulunci na kasar ta fitar.
Zaku iya samun labaran mu a shafin Tuwita @naijcomhausa
&feature=youtu.be
Asali: Legit.ng