Wani mutum ya mutu ya tashi
Shin ana mutuwa a tashine, wani dai ya kwanan dakin gawa
Wani mutumi wanda aka sanar da cewa ya rikaya da ya cika bayan yayi tatil da giya da daddare, ya tashi a dakin ajiye gawawwaki kuma ya dawo cikin jama’a ,wanna ya bawa mutane tsoro.
An bada rahoton cewa wannan abu ya faru ne a Kamienna Gora kasar Poland,inda wani mutum mai suna Kamil ya tashi bayan an fidda rai cewa ya zarce.
Game da cewar Spiesa, labarin ya faru ne lokacin da aka dauki Kamil saboda ya sha barasa na fitar hankali ,ya fadi ya sume kuma aka kaishi asibiti inda aka sanar da cewa ya mutu.
KU KARANTA: Yansanda sun cika hannu da Likitan bogi, amma ƙwararre a harkar tiyata
Amma abun mamakin shine , wani mai gadi a dakin ajiye gawawwakin asibitin yace ya fara jin wasu motsi a cikin dakin ajiye gawawwakin ,kawai sai yaga wani gawa zindir yana neman bargo.
Jaridar Metro UK ta bada rahoton cewa bayan an kira jami’ an yan sanda, an tabbatar da cewa Kamil ne, an gwada shi ,sai aka ce masa ya koma gida.
Asali: Legit.ng