Ɗalibin kwalejin kimiyya ya hallaka budurwasa a jihar Delta
Wata dalibar kwalejin kimiyya da fasaha na jihar Delta ta rigamu gidan gaskiya bayan saurayinta ya kashe ta.
Jaridar Sahara Reporters ta ruwaito cewar an tsinci gawar budurwar ne mai suna Julia a dakin ta dake wajen makaranta, a unguwar Ogwashi-Uku, bayan neman ta da aka dinga yi a daren, amma ba’a san inda ta shiga ba.

Rahotanni sun bayyana cewar ana zargin saurayin Julia da kashe ta, wanda dama dan kungiyar asiri ne, sa’annan rahotanni sun kara bayyana cewar saurayin Julia ya kwana a dakinta, inda har ma ya sace mata katin banki na cire kudi wato ATM, don an gano cewar ya cire makudan kudade daga asusun ajiyarta.
Majiyar mu ta bayyana cewa “bayan saurayin nata ya dauke mata katin banki, sai banki suka aiko mata da sakon ta cirri N100,000 daga asusun ajiyarta, daga nan ne ta gane an sace mata ATM. Ganin haka ya sanya tace bari taje tayi wanka, kafin ta nufi bankin don yin korafi, sai ga shi tana fitowa daga bayi ta kara samun wani sakon an cirri N45,000 duk daga asusun ajiyar ta”
KU KARANTA: Ɗalibin Jami’a yayi barazanar kashe malaminsa

Majiyar ta cigaba da bayani “da tazo zata tafi bankin, sai ta fara jin wani abu a jikinta, sa’anna bayan ta dawo daga bankin, sai tace bankin sun bata tabbacin za’a gane ko wanene ta hanyar amfani da na’aurar daukan hoto, inda suka ce mata ta dawo washe gari”
Majiyar tace farkawar su keda wuya sai kawai suka tsinci gawar Julia bayan sunyi ta kiranta bata amsa ba, don sai da suka balle kofar ta, inda suka ga jini ya malala a ko ina. Tuni dai har a binne Julia, yayin da yansanda ke cigaba da gudanar da bincike.
Zaku iya samun labaran mu a shafin Tuwita @naijcomhausa
&feature=youtu.be
Asali: Legit.ng