An tsinci gawar wani ɗalibi a Sakandaren jihar Yobe

An tsinci gawar wani ɗalibi a Sakandaren jihar Yobe

An tsinci gawar wani dalibin sakandaren gwamnati dake garin Fika ta karamar hukumar Postidkum na jihar Yobe a cikin wani dakin kwanan dalibai da aka dade ba’a amfani da shi ba.

An tsinci gawar wani ɗalibi a Sakandaren jihar Yobe

Jaridar Daily Trust ce ta ruwaito labarin, inda ta bayyana cewar dalibin mai suna Garba Sani ya fita daga aji don yin fitsari a wannan dakin kwana wanda ba’a amfani da shi da misalin karfe 9 na safe, shiru shiru bai dawo ba, sai dai gawarsa aka tsinta a can.

Wani malamin makarantar daya bukaci a sakaya sunansa yayi zargin watakila tursasa ma yaron shiga dakin aka yi, inda aka hallaka shi. Suma daliban makarantar sun ce sun ga wani bakon mutum da suke zarginsa, amma ya haura katangar makarantar ya tsere yayin da suka bi shi.

KU KARANTA: Ya hallaka ɗan uwansa, a zaton sa dabba ne

“Daliban sun bi shi da niyyar kama shi, amma sai ya shige wani gida a kauyen garin Maina, wasu daga cikinsu sun gane shi, sunce tsohon dalibin makarantar ne, amma daga bisani mun samu labarin cewar jami’an soja sun kama shi.” Inji Malamin.

Shima Kaakakin rundunar yansandan jihar ASP Bulus Ndam ya tabbatar da faruwar lamarin, inda yace da misalin karfe 9:30 na safe suka tsinci gawar mamacin. Sa’annan ya kara da cewa a yanzu haka an kama wanda ake zargi ma suna Adamu Yusuf Kunle.

“An ganshi kusa da katangar makarantar jim kadan bayan faruwar lamarin; amma mun fara gudanar da bincike akan shi.” Inji ASP Ndam.

A wani labarin kuma wani dalibin ajin karshe a jami’ar Mkar dake jihar Binuwe yayi barazanar kashe malaminsa saboda ya bashi sakamako mafi karanci a karshen zangon karatu.

Zaku iya samun labaran mu a shafin Tuwita @naijcomhausa

&feature=youtu.be

Asali: Legit.ng

Online view pixel