An kama wata mata a Abuja da yara suna satan kaya a wani b

An kama wata mata a Abuja da yara suna satan kaya a wani b

Wani faifain bidiyo ya watsu ako ina na wata mata mazauniya garin Abuja wacce takeyin amfani da kananan yaranta tana sata kayayyaki a manyan shaguna.

Acewar wanda ke amfani da shafin na Facebook mai suna Don Collins, wanda shine ya sanya bidiyon abun a shafin nasa ya bayyana cewar, andai hangi matar ne tare da yaranta wajan su 7 suna shiga cikin shagon daya bayan daya, inda suka fake da cewar suna neman wasu kayayyakin da babu ma gaba daya a shagon.

An kama wata mata a Abuja da yara suna satan kaya a wani b

Matar kenan tare da yaranta alokacin da suke cikin shagon.

KU KARANTA: Najeriya za ta soma fitar da shinkafa waje a 2017

Haka kuma a hoton, za'a iya ganin inda yaran suka dauki kayan a shagon suna kokarin fita a inda ita kuma mahaifitar yaran ta tsaya gaban mai saida kayan tana kokarin dauke masa hankali a cikin shagon.

An kama wata mata a Abuja da yara suna satan kaya a wani b

Matar tana kokarin dauke hankalin mai tsaron shagon a inda yaran nata kuma suke kokarin satan kaya a shagon.

A inda daya bayan dayan su suka fice daga cikin shagon, inda suka bar mahaifiyar tasu kadai a shagon tana magana dame tsaron shagon, wanda daga karshe ta fita daga cikin shagon bata siya komai ba. In tace bata samu abinda take nema ba.

Allah ya kyauta!

Ku biyomu a shafinmu na tuwita @naijcomhausa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng