Ko ka taɓa ganin masai na Zinari? (HOTUNA)

Ko ka taɓa ganin masai na Zinari? (HOTUNA)

Wani shahararren mawaki, wanda ya kirkiri Cash Money Record mai suna Birdman ya bayyana ma duniya hotunan bayinsa inda ya nuna Tukunyar kashin da yake hawa na Zinari.

Ko ka taɓa ganin masai na Zinari? (HOTUNA)

Attajiri Bryan Williams da aka fi sani da suna Birdman ya bayyana cewar kimanin dala miliyan 2 ya siya tukunyar kashin nasa, kwatankwacin Naira biliyan 9 kenan!

KU KARANTA: Sojoji sun hallaka yan Boko Haram 30 a wata karanbatta

Ko ka taɓa ganin masai na Zinari? (HOTUNA)

Wannan hoto na tukunyar kasha na Zinari ya janyo cecekuce tsakanin jama’a da dama ma’abota kafafen sadarwar yanar gizo musamman na Instagram inda a can ne Birdman din ya nuna ma daya daga cikin yaransa hoton bayin.

Arzikin Birdman na cigaba da habbaka sakamakon nasarorin da yaran kamfaninsa na waka suke samu, yaran nasa sun hada da Lil Wayne, Nicki Minaj, da Drake a yan shekarun nan.

Kalli bidiyon bayin a nan:

zaku iya bin labaran mu a shafin Tuwita: @naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng