Uwa ta hallaka jaririnta, tace sheɗan ne

Uwa ta hallaka jaririnta, tace sheɗan ne

Wata kotu ta saurari kara da aka shigar gabanta na wata mata data hallaka jaririnta, bayan tayi ikirarin yaron Shedan ne.

Uwa ta hallaka jaririnta, tace sheɗan ne

Uwar jaririn yar asalin kasar Senegal ta hallaka jaririn ne bayan tayi ikirarin wani murya daga sama ya fada mata yaronta shedani ne.

Rahotanni sun bayyana cewa a shekarar bara ne matar ta dawo da zama kasar Senegal tare da babbar yarta da mijinta daga Afirka ta kudu.

KU KARANTA: Sojoji sun hallaka yan Boko Haram 30 a wata karanbatta

Sai dai ana zargin matar tana fama da ciwon tabin hankalo da aka fi sani da suna ‘Capragas delusion” wanda ya sanya ta yi ma jaririn nata yankan rago a wata Yulio da ya gabata. Mahaifin ya tarar da matar da yaron kwance cikin jini a kan katifa.

Mahaifiyar jaririn ta bayyana ma jami’in kula da tababbu Richard Furst a satin data haihu cewa bata samun walwala da nishadi, tana cikin damuwa. Tace ta kan ji wasu muryoyi suna fada mata cewa yaronta ba mutum bane, shedan ne, abin da ban tsoro, inji ta.

Sai dai a watan Satumbar data gabat wata kotu ta karyata cewar tana dauke da ciwon haukar a satin data haihu da kuma kwanakin da suka biyo bayan haihuwar tata. Kwanaki biyu kafin ta aikata ta’asan ta fada ma mijinta wai bata jin dadi, amma ta ki zuwa taga likita.

Za'a iya samun labaran mu a shafin Tuwita @naijcomhausa

&feature=youtu.be

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng