Hatsarin Tankar mai ya laƙume mutum daya
Wani mummunar hatsari ya auku a babban titin hanyar zuwa Legas daga Ibadan wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutum guda tare da kona dukiya na miliyoyin naira.
Kimanin shaguna 15 suka babbake tare da motoci 18 sa’ilin da motar tankar mai ta gamu da hatsari a titin Legas zuwa Ibadan bayan wata taho mugama da Tankar tayi da wata babbar mota dake dauke da kayan kwalam da makulashe a mahadar Oremeji a ranar Lahadi 27 ga watan Nuwamba.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewar gaba daya man da Tankar ta dauko ya zube akan titin, hakan ya sanya mutane tserewa daga wurin don gudun kamawar wuta, cikin motocin da gobarar ya shafa akwai manyan motoci 5, kananan motoci kirar Nissan 2, motar bas 2 da suaransu ababen hawa.
KU KARANTA: Kungiyar Izala ta maida martani kan dokar wa'azi
Wani shaidan gani da ido ya bayyana ma The Nation cewar dayar babbar motar dake da lamba JGW 418 XA ne ta kufce ma direban da misalin karfe 7 na safe, inda daga nan sai tayi kan Tankar man, wanda ita kuma nan take ta fadi kasa warwars, daga nan sai gobara ta kama.
Sai dai hatsarin ya janyo cunkoson ababen hawa akan titin, sai da yansanda da jami’an hukumar kare haddura ta kasa, da na hukumar tsaron farin kaya suka kawo dauki don samar da hanyar wucewar mutane, duk da haka sau da aka kwashe sama da awanni 5 ana cunkoso a hanyar.
zaku iya samun labaran mu a shafin Tuwita @naijcomhausa
&feature=youtu.be
Asali: Legit.ng