Wata karuwa ta koma ma mutumiyar kirki
Wata karuwa yar kasar Uganda ta koma wa ubangiji a yayin da tazo coci ta bada kwaroron robar da take amfani da shi gurin karuwanci.
Wata karuwa a kasar Uganda ranar asabar 26 ga watan Nuwamba ta janyo hankalin mutanen da ke cocin a lokacin da ta kawo kwaroron robar da take amfani da shi gurin karuwanci bayan rukiyar da akai mata, a cocin Robert Kenyata Ministry.
Wata budurwa yar shekara 25 Ninsiima Allen ance ta fito daga gurin rukiya a lokacin da ake bauta a coci.
Cocin Robert Kenyata Ministry su ka saka shafin su na Facebook suka ce Ninsiima Allen yar shekara 25 karuwa ce daga Wakaliga.
Ta fita daga karuwanci, ta tuba, ta maida rayuwar ta ga ubagiji.
Nimsiima ta fito daga coci bayan bada kwaroron robar ta da tayi.
KU KARANTA:
Allen ta koma gidan da take sana'ar ta ta karuwanci, ta dauko kwaroron robar ta ta bada, kuma tama yan uwan ta karuwai da su dena abunda suke dan ita ta tuba, ta dena abunda take a da.
Allen ta tsorata da ko ta samu cutar kanjamau a yayin sana'ar ta, amma daga baya da wani cikin malaman cocin mu ya duba ta, sai ya tabbatar mata cewa bata dauke da cutar.
Ta fita karuwanci, ta koma hanyar ubangiji..tsarki ya tabbata ga ubangiji
Allah yasa dai ta dore.
Ku biyo mu a shafin na tuita @naijcomhausa.
Asali: Legit.ng