Jimoh Ibrahim ya taya Akeredolu murna

Jimoh Ibrahim ya taya Akeredolu murna

Jimoh Ibrahim ya taya Chief Rotimi Akeredolu murnan nasarar zabe tun kafin a sanar da sakamakon

Yace Chief Rotimi Akeredolu na jamíyyar APC yayi nasara ne da tazarar kuriú dubu 9, duk da cewan ana cikin kirga kuriú.

Ya bayyana hakan ne a wata wasikar taya murna da ya rubuta ga Chief Rotimi Akeredolu a jiya Asabar, 26 ga watabn Nuwamba.

Karanta wasikar:

Ya kai yayana,

Ina taya ka murna saboda na hada sakamakon da maáikata na suka turo mini a sassa 2907 a jihar Ondo. Ya nuna cewa kana kan gaba da tazara mai fadi.

Ina taya murnan nasarar zabe a matsayin gwamnan jihar mu. Ina baka shawaran cewa ya nisanta daga Mimiko idan kana son nasara.

Banida shakkan cewa zata samar da annashwa ga mutanen mu, kayi kokari ka taimakawa maáikatan gwamnatinmu.

Na ga talauci a idanuwan kauyukan da na je yakin neman zabe ,ka taimakawa sarakunan gargajiya sosai.

Jihar Ondo na bukatan lissafi kuma ya kamata a dawo da kudadenmu da gaggawa domin bunkasa wasu manyan ayyuka a jihar.

Jimoh Ibrahim.

OFR CFR

Dan takaran PDP 2016

Asali: Legit.ng

Online view pixel