Dalilai 5 da yasa yan Arewa ba zasu yadda Atiku yayi shugaban kasa ba
Atiku Abubakar tsohon mataimakin shugaban kasan Najeriya na tsawon shekaru 8 daga 1999- 2007, wanda ya fito daga jihar Adamawa dake yankin Arewacin Najeriya.
Mun dade muna lura da yunkurin Atiku na kokarin dare kujerar shugaban cin kasar nan tun yana matsayin mataimakin shugaban kasa, amma akwai wasu dalilai da suka saka yan arewa ba zasu yadda Atiku yayi shugaban cin kasa ba.
1. Rashin Nagarta
A lokacin da Atiku na matsayin mataimakin shugaban kasa, tsohon shugaban kasa Chif Olusegun Obasanjo ya baiwa Atiku shugaban cin gurin aje kudin rarar mai wato PTDF , Atiku ya dibi kudi $ 300 miliyan da kuma dala$ 164 miliyan daga asusun ya ajiye a Trans International Bank da Equatorial Trust Bank a matsayin bashi kamar yadda EFCC suka tuhume shi a 2006, ya kasance yana samun 15% na ribar kudin , bayan gano lamarin Atiku bai musa ba sai dai yace ya aje aje kudin ne, kuma ya kamata a yaba mashi.
Bayan ribar duk da ya samu a kudin kasa ba nashi ba kuma kan rashin ka'ida, wanda ya saba kudin mulkin kasa.
2. Kabilanci
Yawan mutanen da Atiku ke hulda da su duk sun fito daga yankin sune, wanda a matsayin shugaban kasa ya dace ace kai na kowa ba dan bangare daya ba, dan wannan shi yake kawo tarwatse wa da rashin zaman lafiya a kasa.
3. Rashin gaskiya da yaudara
Tun daga abubuwan da muka gani a lokacin mulkin Obasanjo mun gano cewa Atiku ba wai yana son shugaban cin kasa bane dan yan Najeriya yana yine dan gashin kansa, duk da a kwanan baya munga an nuna Atiku yana shan ruwan leda, wanda yana kokarin nuna ma yan Najeriya cewa Shima ze kwatanta irin rayuwar su.
4. Kasar Amurka tana neman sa
Akwai tabbacin cewa kasar Amurka suna neman Atiku kan almun dahana, an ce ya hada kai da wani dan kasar gurin yin almun dahana da bannatar da kudin kasa, wanda yanzu Atiku kasar ta Amurka ta haram ta ya shiga, duk ya musanta haka a in da yace ba yada iyali a kasar shiyasa ya dena zuwa, kunga kuwa ba zamu so shugaban da wata kasa ke nema ba ruwa jallo kan handamar kudin kasa.
5. Me Atiku za yi wanda Buhari ya kasa yi a shekarun shi a halin yanzu.
Atiku ze yi takarar 2019 yana da shekara 73, kamar yadda Buhari yake, a wannan shekaru in dai har ana zagi da ganin laifin Buhari banga dalilin da za'a dora Atiku dan bamu san me zeyi ba a wadan nan shekarun.
Ku biyo mu a shafin mu na tuita @naijcomhausa
Asali: Legit.ng