Al’amuran ban mamaki 10 dake cike da rayuwar Atiku

Al’amuran ban mamaki 10 dake cike da rayuwar Atiku

- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya cika shekaru 70 da haihuwa

- Jam’iyyar APC ta taya Alhaji Atiku Abubakar murna, tace sune Najeriya da kuma tsohon mataimakin shugaban kasan yayi hidima wajen inganta rayuwa da siyasar al’umma

Al’amuran ban mamaki 10 dake cike da rayuwar Atiku

Tsohon mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar ya cika  shekaru 70 a duniya, Jam’iyyar su ta APC ta taya sa murnar wannan rana. APC tace ba zai yiwu a rubuta Tarihin Najeriya ba tare da sunan Atiku ba.

APC tace Atiku Abubukar ya inganta rayuwar ‘Yan Kasar nan ta fannin mu’amala, zaman siyasa, tattalin arziki da cigaban al’umma. APC tace Atiku mutum ne wanda aba ruwan sa da bambancin kabila ko yare.

Ga wasu abubuwan ban mamaki 10 na tarihi da rayuwar Atiku take cike da su nan da Legit.ng muka kawo maku:

1. An haifi Alhaji Atiku Abubakar ne a 25 ga watan Nuwambar shekara ta 1946. Wannan ne yake nuna cewa shekarar sa 70 da haihuwa yau cif.

2. Atiku Abubakar shahararren dan siyasa ne kuma dan kasuwa mai yawan kyauta da taimako. Ya yi zama a matsayin mataimakin shugaban kasar Najeriya daga shekara ta 1999 zuwa ta 2007 a karkashin jam'iyyar PDP.

3. Kafin nan dai shi Atiku Abubakar ya yi aiki da hukumar Kwastam ta kasa har na tsawon shekaru 20 inda har sai da yazama mataimakin Darekta a hukumar kafin daga bisani a yi ritaya.

KU KARANTA: Wani Bahaushe ya kafa tarihi a kasar Amurka

4. Alhaji Atiku Abubakar ya ajiye aikin sa da hukumar Kwastam a watan Afrilun shekara ta 1989 sannan ya maida hankalin sa kacokam kan harkar kasuwancin sa da kuma sinaya.

5. Atiku Abubakar yayi takarar gwamnan jihar Gongola wadda ke zaman jihohin Adamawa da Taraba yanzu a shekara ta 1991 a jam'iyyar SDP sannan kuma yayi takarar fidda gwani ta shugaban kasa a shekara ta 1993 duk a SDP din.

6. A shekara ta 1998 Atiku Abubakar ya ci kujerar gwamnan Adamawa amma sai daga baya kuma aka zabe shi don ya zama mataimakin shugaban kasa a karkashin jam'iyyar PDP tare da Cif Obasanjo. Wannan ne ma yasa aka rantsar da su a ranar 29 ga watan Mayun shekarar 1999 bayan sunyi nasarar cin zaben.

7. Atiku ya so ya zama shugaban kasa bayan Obasanjo wanda kuma hakan bai samu koyon bayan shugaban kasar a wancan lokacin ba. Rikin da ya jawo har hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC ta haramnta masa tsayawa takara amma daga baya sai kotun kolin kasar ta wanke shi daga dukkan zargin.

8. Daga bisani Alhaji Atiku ya tsaya takara a karkashin jam'iyyar AC bayan ya fice daga jam'iyyar PDP a shekara ta 2007.

9. Atiku ya sha kaye a zaben da aka gudanar a shekarar ta 2007 inda yazo na 3 bayan tsohon shugaban kasa marigayi Alhaji Ummaru Musa Yar'adua da kuma shugaban kasar Najeriya a yanzu Muhammadu Buhari.

10. Atiku Abubakar ya na da manyan kamfanoni da dama a ciki da wajen kasar nan ciki kuwa hadda 'Intels' wanda suka shahara wajen harkokin mai da kuma Adama Beverages Limited dama jami'ar American University of Nigeria (AUN).

&feature=youtu.be

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng