Wani dan dambe ya mutu

Wani dan dambe ya mutu

Kuba Moczyk , dan wasan dambe wanda ya samu rauni a kai a wasar shi ta farko ya mutu a asibiti, BBC ta ruwaito.

Wannan lamarin yan uwan shi suka bayyana faruwar shi, wadanda suka ce ya mutu daren laraba 23 ga watan Nuwamba a asibitin James Paget a garin Gorleston, inda yake a sume, yana shakar numfashi da taimakon na'urar numfashi.

Dan shekara 22 an cire shi a zagaye na 3 na wasar dambe ranar asabar a filin Tower Complex, na garin Yarmouth kasar England.

Wani dan dambe ya mutu

Kamar yadda mai shirya gasar Leon Dowra ya bayyana yace" za'ayi shiru na dakika 1 kan mutuwar Moczyk kafin fara wasar asabar da za'ayi da tsohon wanda ya lashe gasar a garin Gorleston ranar alhamis da dare.

"Nayi waya da Tyson jiya da dare, kawai da safiyar nan sai naji mummunan labari" inji Docwra.

Docwra wanda ya koya ma Moczyk damben na kusan shekara 3, yace yana da zuciya mai kyau.

KU KARANTA: 

Ba ze zama zakaran duniya ba a wasar dambe, amma dai yana da kirki, kuma zuciyar shi tana da kyau. Ka kasance cikin masu wasar dambe, babban abu ne a rayuwa,kuma kowa yana alfahari da shi.

Docwra yace ya hana yaran shi wasar dambe yan shekara 11 da dan shekara 16 saboda mutuwar Moczyk.

Ainahin Moczyk dan kasar Poland ne , yana aiki a ma'aikatar Kaji, kuma yana zama a garin.

Abokin damben nashi wanda ya doke shi ance dan shekara 17 ne.

Ku biyo mu a shafin mu na Tuita@naijcomhausa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel