Wata tsohuwa ta bayyana yadda take harkokin maitar ta a coci

Wata tsohuwa ta bayyana yadda take harkokin maitar ta a coci

Wata tsohuwa ta bayyana wani abu mai ban al'ajabi a cochi dangane da ita karan kanta a ranar Lahadi 20 ga watan Nuwamba.

Tsohuwar dai ta bayyana cewar ta kwanta da yaron ta na cikin ta duk a harkar tsafin da takeyi na maitar ta. Tsohuwar dai wacce ba'a bayyana sunan taba, ta bayyana wannan abun ne a cochin nan na Zimbabwean Prophet Sham Hungwe’s House of Grace International Ministries, alokacin da ake gudanar da addu'a.

Wata tsohuwa ta bayyana yadda take harkokin maitar ta a coci

Tsohuwar data bayyana abu mai ban mamaki a lokacin da ake gudanar da addu'a a cochi a ranar Lahadi 20 ga watan Nuwamba.

Haka kuma, ta bayyana karara a fili cewar, tayi harkar mayinta sosai, inda ta cinye mutane kimanin 70 wanda suka hada hadda yarinyar ta ta cikin ta, da kuma sauran yan uwan ta.

KU KARANTA: Abubuwan da ‘yan Najeriya suka tattauna akai jiya Alhamis (Karanta)

Inda ta bayyana cewar " Nina fara sanya yaro na ya fara sanin meye ya mace, saboda na sanya yarona ya sadu dani akwanakin baya. Saboda babu yadda zanyi saboda yana daga cikin sharuddan yin haka a harkar tamu ta tsafin. Na dade acikin wannan harkar ta maitan, inda na cinye mutane a kalla 70, sannan kuma nina kashe yarinyata da kaina, kuma nine dalilin duk wani rashin sa'a da tsautsayin da yake faruwa akan yarana". Inda take fadi a gaban daruruwan mutanen dake cikin cochin.

Wata tsohuwa ta bayyana yadda take harkokin maitar ta a coci

Tsohuwar dai wacce ba'a bayyana sunan taba, ta bayyana wannan al'amarin ne a cochin Zimbabwean Prophet Sham Hungwe’s House of Grace International Ministries alokacin da ake gudanar da addu'a a cochin.

Meturon cochin ta bayyana cewar tsohuwar datazo daga wani gari da ake cema Murewa, tadai samu rakiyar wasu yan uwanta alokacin da tazo cochin domin ta fallasama jama'a irin mugayen abubuwan datayi a baya. Sai dai kuma limamin cochin mai suna Hungwe, ya bayyana ma jama'a cewar yanada kwarewar da zaiyi ma mutum addu'a domin ya rabu da harkar tsafi da kuma maita. Inda yayi mata addu'a kuma ya tabbatar da tubarta ga jama'a.

Hmm, Allah ya kyauta!

Ku biyomu a shafinmu na tuwita. @naijcomhausa

 

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng