Yaro ďan shekara 3 ya ceci rayuwar mahaifinsa
Wani karamin yaro mai shekaru uku yayi bajinta yayin daya tilasta ma babansa shan madara bayan ya yanke jiki ya fadi a gida.
[caption id="attachment_1060668" align="alignnone" width="300"] Lenny da Babansa[/caption]
Mahaifin yaron Mark Jones ya fadi ne a dakin girkin gidansu sakamakon ciwon siga data harbe shi a lokacin, ganin haka sai ďansa Lenny George yayi wuf ya hau kan kujera inda ya bude na’urar sanyaya abinci ya dauko kwalayen madarar yogot guda biyu.
Daga nan sai yaron ya sake komawa ya dauko wukar roba wanda yayi amfani da ita wajen dura ma mahaifin nasa madarar a baki har sai daya dawo cikin hayyacinsa. Sa’annan ne uban ya iya gane halin dayake ciki, inda nan da nan ya je ya sha magani.
KU KARANTA: Wani yaro yaci duka a hannun Mariƙinsa
Mahifiyar Lenny Geroge, Emma ta bayyana farin cikin ta yadda hazikin yaron ya nuna bajinta, inda tace da labara ya sha banban da ba don yaron ba Emma daga fitar ta zuwa gidan Mahaifiyarta wanda bai fi mintuna 30 ba lamarin ya faru.
“Da na dawo sai naga Mark ba lafiya,” inji matarsa, “sai na tambaya ko lafiya?” Sai Lenny yace min “na cece rayuwar baba.”
Marka yace “gaskiya ne,” Emma tace duk da cewar basu taba fada ma yaron rashin lafiyar dake damun babansa ba, amma ya iya yin tunani taimakon baban. Wata kila saboda yana ganin yadda nake yi ne idan mahaifin nasa ya shiga wannan halin.
Zaku iya tuntubar mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa
&feature=youtu.be
Asali: Legit.ng