Matar da ta fi kowa tsawon farce da sauransu

Matar da ta fi kowa tsawon farce da sauransu

Ga jerin wasu mutane da Allah Ya yi musu baiwa ta halittar da ta zarce kowa a duniya,wasu kuma tattalin abin suka yi domin shiga kundin tarihi.

Matar da ta fi kowa tsawon farce da sauransu

1. Farce: Matar da tafi kowa tsawon farce a duniya a shekarun 2009 ita ce Lee Redmond, tsawon farcen wannan mata ya kai mita 8.5, sai a kimanin shekaru 7 da suka wuce Lee ta yi hatsari a inda ta rasa faratun nata na hannu da kafa da kuma wannan matsayi a duniya.

2. Hanci: Mutumin da ya fi kowa tsawon hanci a duniya dan kasar Turkiyya ne, tsawon hancin na sa ya kai santimita 7.

3. Kafa: Matar da ta fi kowa tsawon kafa a duniya wata ‘yar kasar Rasaha ce, mai suna Svetlana Pankratova, Allah Yayi wannan mata baiwar tsawon kafa da ya kai santimita 132!

4. Farcen kafa: Wacce ta fi kowa tsawon farcen  kafa kuwa wata ‘yan Amurka ce mai suna Louise, tsawon facenta na kafa ya kai mita 2.5, tana kuma da ‘ya ‘ya 12 da jikoki 21, amma duk da haka ta iya kiyaye faratunta na kafa ba su karye ba. Aiki sai mai shi!

Matar da ta fi kowa tsawon farce da sauransu
Lauren Williams ita ce ta fi kowa tsawon kafa a Amurka

5. Wuya: Matan kasar Burma sun yi fice a wajen gasar tsawon wuya. A bisa al’adar mutanen wannan kasa, mace ba ta cika mace ba, idan ba ta da dogon wuya. Hakan ya sa ‘yan mata da ga kananan shekaru suke sa wasu zabba a wuya, wanda suke girma da su har iya tsawon rayuwarsu domin sun amsa sunan kyakkyawa.

6. Gashin ido: Wanda ya ke rike da wannan matsayin na wanda ya fi kowa tsawon gashin ido a duniya kuwa, shi ne Valeriy Smagliy, dan kasar Ukraine. Ya kuma samu nasarar kaiwa ga wannan matsayi ne, sakamakon tsawon gashin idanunsa da ya kai santimita 3. Ba dai bayyana sirrin yadda ya ajiye ba.

Matar da ta fi kowa tsawon farce da sauransu

7. Tsawon Gashin kai: matar da ta fi kowa tsawon gashin kai a duniya ita ce Xi Qiping wacce tsawon gashin kan ta ya kai tsawon mita 5.63.

Ko me zaka ce dangane da wannan labari? Garzaya shafinmu na Tuwita a @naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng