Tirkashi!!! Wani direba ya haukace bayan yaci abinci a Ibadan

Tirkashi!!! Wani direba ya haukace bayan yaci abinci a Ibadan

Wani Fasto mazauni Ibadan Gideon Johnson ya bayyana wani labari mai tsoratarwa na yadda direban shi ya haukace bayan ya ci abincin da matar Faston ta dafa.

Faston ya bayyana labari mai tsoratarwa a kotun Grade C Customary dake garin Agodi-Ibadan, a lokacin da yake kaunar a raba shi da matar sa da suka yi shekara 17 a tare.

Yace mata ta, ta so ta saka ni in haukace, amma cikin hukuncin ubangiji sai ya kare ni abun ya fada ma direba na bayan gama cin abincin, yayin da yake zargin matarshi kuma uwar yaran shi guda 4 kan tana da tabin hankali, Johnson yana cewa matar shi bata da hali nagari, dan haka kuma yace barazana ce a rayuwar shi da sauran iyalin sa.

Tirkashi!!! Wani direba ya haukace bayan yaci abinci a Ibadan

Yace" Direban da be ji bai gani ba ya haukace yan awanni kadan bayan gama cin abinci, dan haka mun daure shi da kaca kafin mukai shi gurin iyalin shi da neman mafita, ta so ta bata man rayuwa, ita mayya ce, muguwa, kuma barazana a rayuwa ta, a takaice dai ta kashe yaya na da baba na a cikin maitar ta.

KU KARANTA: 

Saura kadan ta bata man rayuwa, dan ta hada kai da makiyana dan sun kunyatar dani gaban Mambobin coci na, na kaurace mata na tsawon shekara 11 saboda munanan halayen ta, kuma ina tabbatar maku da zan kashe ta in ba'a raba auren ba.

A lokacin da take kokarin kare kanta tace'" be damu dani ba haka ma yayan sa 4, sai da kullum yayi ta zagina a gaban Mambobin cocin sa, yana kuma zargi na nace wa ni mayya ce, kuma na kalubalance shi da yayi man rukiya tun da shi Fasto ne.

Ban kashe mai dan uwa ba ko mahaifi, miji na ya zubar damu na tsawon shekaru 11, bayan auren wata mata da yayi da ta haifa mai yara 3, ina rokon kotu da kar ta raba mana aure ko dan yaran da ke tsakanin mu.

A lokacin da yake yanke hukuncin mai shari'a Bologun Mukaila ya raba auren , kuma ta bada umurnin yara 3 su kasance gurin wanda ya kawo kara, sauran kuma yaran 2 suje ga mahaifiyar su.

Kuma ya bada umurnin cewa mai karar ya rika bada dubu 8 duk wata na kula da yaran shi da ke hannun matar, sai dubu 12 da zata kama haya, sai kuma dubu 5 da za'a bata ta kwashe kayanta daga gidan wanda ya kai kara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng