An kama wasu ma'aurata suna saduwa gaban yaro
Wasu ma'aurata daga Connecticut kasar Amurka, sun ba dimbin mutane mamaki kan mummunar dabi'a da suka yi bayan kama su da akayi suna saduwa a gaban yaro dan shekara 6.
Ma'auratan masu suna Kimberly Onarato da mijin ta Rory Clark an kama su bayan ganin su da akayi suna saduwa a wani gurin aje mota a gaban yaro dan shekara 6 da yake aje a cikin abun goya yara a wajen Mcdonald.
Jaridar Daily UK ta ruwaito cewa yan sanda daga yankin Town of Orange sun nuna cewa lamarin ya faru ne kafin karfe 9:40 na yammacin 15 ga watan Nuwamba a wajen wani gurin cin abinci Fast foot mai adireshi lamba 57 hanyar Orange .
KU MARANTA:
Ma'aikatan McDonald's guda 2 sun fito daga aiki a dai dai lokacin suka ci karo da wadan nan ma'auratan suna aika-aikar su a gurin zama na gaba a motar su, shi kuma yaron yana baya ido kiri yana kallon su a yayin da suke tafka ta'asar su.
Lokacin da yan sanda suka ji lamarin, sun samu Kimberly Onarato yar shekara 28 kusan tsirara, amma a lokacin da ake masu tambayoyi , Onarato da Rory Clark sun ce kawai sun rike juna ne kawai bayan gama cin abinci.
Sai dai an zargin su da karya doka ta 2 ta hakkin kananan yara da tada zaune tsaye, shi kuma yaron dan shekara 6 an maida shi ga yan uwan shi, haka kuma yan sanda sun sanar da lamarin ga hukumar kula da kananan yara da iyayen shi, ba wanda ya san alakar yaron da ma'auratan har yanzu.
Asali: Legit.ng