Batutuwan da suka shahara a jiya Laraba

Batutuwan da suka shahara a jiya Laraba

Jaridar Legit.ng ta tattaro muku batutuwan da Najeriya suka tattaunawa a jiya Laraba, 23 ga watan Nuwamba

1. Rashin kunya ne gwamnatin PMB ta rika yin maganar 2019 - Mohammed

Batutuwan da suka shahara a jiya Laraba

Mohammed yace gwamnatin Buhari na kwadan mulki, yaudara da cin rashawa har ta fara yin maganar 2019 bayan babu abinda tayi cikin shekara daya da rabi kan mulki.

2. An gano badakalar N2.175 billion a ma'aikatar tsaro

Batutuwan da suka shahara a jiya Laraba
Arms deal scandal

Kwamitin shugaban kasa akan binciken badakalar makamai ta gano wata kudi N2.175 billion a daya daga cikin ma'aikatan ma'aikatar tsaro. Kudin wanda aka bayar a sayi makamai da shi an karkatar.

3. An ceto mata 8 da yara daga hannun Boko Haram a Sambisa

Wasu mafarauta sun ceto mata 5 da yara 3 daga hannun yan Boko Haram a dajin Sambisa. Jaridar Premium Times ta bada rahoton cewa, Garba Tarfa, shugaba yan farauta a jihar Adamawa yace a ceto su ne a makon da ya gabata.

4. Sifeton yan sanda ya damu akan mutuwan hafsoshi 128

Batutuwan da suka shahara a jiya Laraba

Sifeto-Janar nay an sanda, Ibrahim Idris yayi matukar nuna damuwarsa akan mutuwan hafsoshin yan sanda.

5. Gobara a jamíar Yabatech

Batutuwan da suka shahara a jiya Laraba

Rahotanni da muke samu daga makarantan Yaba College of Technology (Yabatech), a jihar legas na cewa dakin kwanan dalibai na Bakassi na ci da gobara.

6. Anyi rashin rayuka 11 a rikicin ‘yan sanda da mafarauta

Batutuwan da suka shahara a jiya Laraba

Jaridar The Nation ta bada rahoton cewa Mutane 11 ne suka rasa rayukansu a wata mumunan rikicin da ya auku tsakanin yan sanda da mafarauta a Ogbere Onilanta karamar hukumar Ona-Ara a jihar Oyo.

7. Tinubu na nan da rai da koshin lafiya -Afikuyomi

Babban jigon jam'iyyar APC,Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, nanan fikin koshin lafiya game sa cewar wani mai aikinshi Sanata Tokunbo

Ku biyo mu a shafinmu na Tuwita: @naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng