An tsirar da mata da yara guda 8 daga hannun boko haram
- Wasu mafarauta a Adamawa sun tsirar da wasu mata da yara guda 8 daga hannun Boko Haram dake dajin nan mai hadari na Sambisa
- Matan da yaran an kai so gurin hukumomin tsaro dan kai rahoto
Wasu jaruman mafarauta sun tsirar da mata 5 da yara 3 daga hannun yan ta'addan boko haram da ke kame a dajin Sambisa.
Jaridar premium times ta ruwaito mana cewa, Garba Tarfa shugaban kungiyar mafarautar na jahar Adamawa yace wadanda suke kamen an tsirar da su makon da taci gabata.
Mutanen mu sun tsirar da matan da yaran makon da ya gabata dai dai sun fito da gudu, yayin dauki sojojin mu suke dauki ba dadin barin wuta da yan boko haram.
Tarfa yace" a halin yanzu dai mun kai matan da yaran gurin hukumar da ta dace dan basu kulawa ta musamman, sun bada labarai mara dadi a kan dajin Sambisa.
KU KARANTA: Babban dan wasan duniya zai shiga kurkuku.
Tsiratar da wadan nan mutanen 8 yazo mako 1 da tsirar da wasu mutane 14 wanda mafarautar yan banga suka yi a yayin barin wuta tsakanin sojoji da yan kungiyar ta boko haram.
Mai magana da yawun bakin yan sanda na shiyar Adamawa ya tabbatar da ceto su da akayi, lalle munji cewa mafarautan sun tsirar da su, amma har yanzu ban samu cikakken bayani ba.
In zaka iya tunawa Boko Haram sun saki yan matan chibok 21 bayan yarje-jeniyar da suka yi da gwamnati.
Duk da yake har yanzu ba muji taka mai man abunda aka tattauna a yarje-jeniyar kafin sakin yan matan.
Asali: Legit.ng