Mafarauta sun kubutar da wasu da Boko Haram suka sace

Mafarauta sun kubutar da wasu da Boko Haram suka sace

Matan da yaran da mafarautan suka ceto daga dajin Sambisa inda kungiyar Boko Haram ta yi kakagida an sacesu ne yau fiye da shekaru biyu kuma abun tausayi shi ne yaran makarantun firamare suke lokacin da 'yan ta'adan suka sace su.

Kamar dai yadda bayanai ke nunawa, wadannan mata da yara sun samu kubuta ne daga dajin Sambisa biyo bayan fafatawan da dakarun Najeriya ke yi da mayakan Boko Haram,inda daga bisani yan sakai na maharba suka ceto su.

Tuni ma dai aka iso da wadannan mata zuwa Yola,fadar jihar Adamawa domin mika su ga jami’an tsaro.

Mafarauta sun kubutar da wasu da Boko Haram suka sace

Daya daga cikin matan da aka ceton Malama Aisha,mai kimanin shekaru 20 ,wadda yan Boko Haram suka sace yau fiye da shekaru biyu a Gulak dake karamar hukumar Madagali tace sun ga tasku a hannun yan Boko Haram.

Kamar Aisha suma wasu kananan yan matan dake makarantar Firamare ,wadanda basu fi shekaru 13 zuwa 15 ba, sun bayyana cewa yan Boko Haram sun yi musu auren dole. Kuma kawo yanzu akwai dinbin kananan yara dake hannun yan Boko Haram a dajin Sambisa.

Batun yau ba ne dai 'yan sa kai na maharba ke tallafawa sojoji ,musamman a yankunan da aka kwato daga hannun mayakan Boko Haram,inda 'yan sakan kan shiga daji don zakulo burbudin 'yan bindiga masu tada kayar bayan.

Garba Tarfa dake zama jami’in harkokin tsaro da bincike na kungiyar maharban jihar Adamawa,ya ce kusan wannan ne karo na biyar da suke ceto mata da kananan yara da 'yan Boko Haram suka sace.

Kawo yanzu dai hukumomin tsaro basu yi cikakken bayani ba game da matakin da za’a dauka game da matan da kananan yaran da aka ceton,to amma kuma rundunan yan sandan jihar Adamawa tabakin kakakinta SP Othman Abubakar yace tuni suka kara tura jami’ansu yankunan da aka kwato tare da yin kira ga jama’a da su bada hadin kai,don kwalliya ta biya kudin sabulu, a fafutukan da ake yi na kawo karshen matsalar Boko Haram.

&feature=youtu.be

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng