Muhimman batutuwan ranan talata (karanta)
Jaridar Legit.ng ta tattaro muku muhimman batutuwan ranan Talata, 23 ga watan Nuwamba
1. Yadda aka kusa garkuwa da Mamman Daura
Jaridar Premiuim times ta tattaro labara cewa yan bindigan da sukayi garkuwa da Bagudu Hirse,tsohon minista, bas hi sukayi niyyan daukewa ma, ainihi Mamman Daura ne akayi niyyan yin garkuwa da shi.
2. Kalubale 5 da shugaba Buhari ke fuskanta
3. Shugaban jamíyyar APC ya kwanta dama
A lokacin da muke tattara wannan rahoto, babu cikakken bayanai akan rasuwarsa,amma jaridar Punch ta bada rahoton cewa daya daga cikin yaransa ,Bolaji Adeniyi, yace mahaifinsa wanda akafi sani da ‘Baba Computer’ya rasu ne a daren ranan litinin,21 ga watan Nuwamba.
4. Mu zamu zabi shugaban kwamitin amintattu– Gwamnonin APC
Hayaniyan da ke faruwa tsakanin shugaban APC, Chief John Odigie-Oyegun,da babban jigon APC, Asiwaju Ahmed Tinubu ta dau sabon salo.
5. Talauci kafiri ne: Wani mutum yayi zindir a tsakiyan hanya a jihar Legas
Wani abun kallo da mamaki ya faru a yau a jihar Legas, yayinda wani mutum mai shekaru isasshe ya tube kayansa zindir cikin jamaá babu kunya babu tsoron Allah.
6. Orji Uzor Kalu dukiyar siyasa ne - Gwamna Okorocha
Gwamna Rochas Okorocha na jihar Imo ya bayyana tsohon gwamnan jihar Abiya basarake Orji Uzor Kalu a matsayin arziki a siyasance, cewar rohoton The Punch.
7. Rundunar sojin sama sun yi ma Boko Haram ruwan wuta
A wata jawabin da ta daura a shafin ta na sada raáyi da zumunta, rundunar sojin samar ta tabbtar da labarin yadda sukayi amfani da jirgin sama wajen tarwatsa wasu yan boko haram inda suka ganawa a ranar laraba, 16 ga watan Nuwamba.
8. Najeriya ce matalauciyar kasa ta 3 a duniya- Credit Suisse
Sun bada rahoton cewa Najeriya ce kasa matalauciya ta 3 a duniya saboda tana da mutane 35million mafi talauci a fadin duniya. Kasar Indiya ce matalauciyar kasa ga baki daya.
ku biyo mu a shafinmu na Tuwita :@naijcomhausa
Asali: Legit.ng