Jinjinawa ga sojojin Najeriya saboda...

Jinjinawa ga sojojin Najeriya saboda...

- Kwamandan rundunar Birgediya Janar Benson Akinreleyo ne ya jagoranci bikin mika kayan gudumawar na koyaswa

- Rundunar sojoji ta 23 dake Yola, fadar jahar Adamawa ta mika gudumawar kayan karatu ga malamai da suke karantar da 'yara 'yan gudun hijira, wadanda rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu fiyeda shekaru 6 yanzu

Jinjinawa ga sojojin Najeriya saboda...
Sojojin Najeriya

Ku Karanta: Rundunar sojoji ta kama wani sojan bogi

Kwamandan rundunar Birgediya Janar Benson, yace baya ga yaki da 'yan binidga masu tada kayar baya, dakarun kasar suna kuma tallafawa 'yan gudun hijira ta fuskar kiwon lafiya, da ilmi, da kuma tabbatar da wadanda suka sami komawa muhallansu basu fuskanci matsi ba.

A hukumance hukumar bada agajin gaggawa watau NEMA ce take kula da 'yan gudun hijira. Mallam Sa'adu Bello yace, shirin samar da ilmi da hukumar take baiwa 'yan guudn hijiran, yana taimakwa yara masu yawa. Domin a karon farko akwai wadanda basu taba shiga makaranta ba da suke cin gajiyar shirin.

A wani labarin kuma dai Yayin da dakarun sojin Najeriya ke ci gaba da fatattakar mayakan kungiyar Boko Haram a yankunan dake dajin sambisa, yanzu haka mayakan na karkatawa zuwa wasu kauyukan da babu sojoji.

Hari na baya bayan nan da suka kai shine wani harin sari ka noke da suka kai wasu kauyukan karamar hukumar Madagali, dake makwabtaka da jihar Borno, inda baya ga asarar rayuka kuma suka sace Shanu tare da lalata gonaki.

 

A biyo mu a shafin mu na Tuwita @naijcomhausa

&feature=youtu.be

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng